Idan wayarka na da wata daraja a wurinka... wannan rubutun yana iya cetonta!

0
455

Idan wayarka na da wata daraja a wurinka... wannan rubutun yana iya cetonta!

 

Lokacin zafi ba wasa bane, ka sani wayarka ba ta da karfin jure zafi kamar yadda kai kake ɗauka.  

 

Kowane minti da take ƙarƙashin rana = rayuwar batir ke raguwa kuma da wayar keyi zai ɗan yi rauni. 

 

Ka daina ɗaukar zafi da wasa, ba wai hanging kaɗai zata yi ba…  

 

Zai iya sa ta daina aiki gaba ɗaya, rage tsawon rayuwarta, ko abu mafi muni… ta iya kamawa da wuta!  

 

Idan kuma ka lura da wayarka tana ɗaukan zafi da wuri ko batir ɗinta na ƙarewa da wuri, to, wannan rubutun naka ne. Karanta shi har karshe:

 

Yadda zaka kare wayarka daga gobarar zafi:

1. Ka dinga kiyaye ta daga zafin rana kai tsaye:

Ka daina sata kan dashboard na mota, gefen taga, ko cikin aljihu da rana, duk yana ƙara zafin ta.

 

2. Ka rage nauyin da kake ɗora mata:  

Idan ba ka buƙatar Bluetooth, Wi-Fi ko GPS kashe su. Waɗannan suna fitar da elektiriti da kuma ƙara zafi mata zafi. 

 

3. Rufe apps masu nauyi:  

Wasanni na games, camera, da sauran manyan apps ka dinga hakuri da su, musamman a cikin rana.

 

4. A cire case ɗinta lokaci-lokaci:

Case na hana waya shan iska, ka dinga bari tana shan iska lokaci lokaci. 

 

5. Idan ta ɗau zafi sosai, kashe ta na ƴan mintuna: Ba fa laifi bane ajiye waya a kashe na ɗan lokaci dan ta ɗan huta, yin haka yana ƙara mata rai!

 

Kada zafin rana ya lalata wayarka. ka kula da ita kamar yadda kake kula da kanka!

 

Idan wannan post ya amfane ka, tura shi wa wanda kake so… domin zai iya ceton wayarsa ko rayuwar su!

Zoeken
Categorieën
Read More
Networking
How I Started My VTU Business – And How You Can Too!
  How I Started My VTU Business – And How You Can Too!   I started my VTU...
By Fodiyo Aminu 2025-07-16 01:55:49 0 465
Networking
Starting Your Own VTU Business: A Beginner’s Guide
    Starting Your Own VTU Business: A Beginner’s Guide   So, you’ve...
By Fodiyo Aminu 2025-07-16 03:13:25 0 457
Networking
Idan wayarka na da wata daraja a wurinka... wannan rubutun yana iya cetonta!
Idan wayarka na da wata daraja a wurinka... wannan rubutun yana iya cetonta!   Lokacin zafi...
By Fodiyo Aminu 2025-07-18 00:18:39 0 455
Sauri https://sauri.ng